Easy Shinkafa mai kayan lambu da miyar kayan ciki da dankali Recipes

Easy Shinkafa mai kayan lambu da miyar kayan ciki da dankali Recipes

The ingredients Easy Shinkafa mai kayan lambu da miyar kayan ciki da dankali Recipes

 1. 4 Shinkafa Kofi
 2. Kara’s
 3. Koren wake
 4. Koren tattasai
 5. Koren fis
 6. Albasa
 7. Ataruhu
 8. Kayan dandano
 9. Kayan kamshi
 10. Dankalin turawa
 11. Kayan cikin shanu
 12. Tattasai
 13. Tafarnuwa
 14. Citta

Step-step making Easy Shinkafa mai kayan lambu da miyar kayan ciki da dankali Recipes

 1. Ki wanke shinkafanki saiki tafasa ta ki kara wanketa saiki maidata wuta kisa gishiri da dan ruwa kadan ki kara turara ta, saiki sauke ki barta tasha iska sosai.

 2. Ki wanke kayan lambu saiki yanka yanda kikeso.

 3. Kisa mai yay zafi saiki zuba cotta da tafarnuwa, karas, koren wake, albasa rabi, fis, kayan dandano da ataruhu ki juya saiki zuba shinkafan da albasa rabin da koren tattasai ki juya a hankali saiki bar ta turara.

 4. Idan tayi saiki sauke kasa ki kawo foil paper ki daura akan shinkafan saiki zuba garwashi kadan Ki barbada mai cokali daya akan garwsshin zakiga ya fara hayaki saikiyi saauri ki rufe saboda anason hayakin ya shiga cikin shinkafan kamar minti biyar.

 5. Ki fere dankalin ki saiki tafasashi a guda gudanshi.

 6. Ki wanke kayan ciki saiki barshi ya tafaso saiki wanke shi tas sannan Kisa mashi kayan dandano da Albasa, kayan kamshi da ruwa ki barshi ya fara dahuwa saiki zuba jajjagaggen kayan miyanki da dankalin ki barsu su nuna.